HAUSA LANGUAGE THIRD TERM JS 1(BASIC 7)
THIRD TERM E- LEARNING NOTES
JS 1(BASIC 7)
HAUSA LANGUAGE
SCHEME OF WORK
WEEK TOPIC
- Kayayyakin amfani a gida
- Ire-iren kayayyakin da ake amfani dasu a gida
- Kayayyakin amfani na cikin daki
- Kayayyakin anfani na tsakar gida
- Kayayyakin amfani na yin girki
- Ma’anar furuci.
- Gabobin furuci
- Gabobi masu motsi
- Gabobi marasa motsi.
- Ma’anar gina kalma
- Bita akan darasunnan sashe duka
- Jarrabawar sashe
Week 1 Kayyakin da ake amfani dasu a gida.
Kamar yadda muka sani a darusan mu dasu ka gabata munyi bayani
akan tsarin gidan bahaushe. Bayani ya nuna mana yadda bahaushe ya tsara gidan sa fara daga zaure, Katanga, dakuna da tsakiyar gida.
Abubuwa da suke cikin gida sunhad da; Gado, katifa, matashin kai, kujerar zama, taburma, randa, daki, tsakarkari, kayayyakin sawa, tukwane, kwanuka kayan abinci, rumbu d.s.
Kayakin da ake amfani dashi a gida sun kasu iri-iri.
Ire-iren kayakin da ake amfani das u wajen kwanciya
- Gado
- Taburma
- Katifa
- Mayafi
Kayakin da ake amfani dasu a daki
- Kujerar zama
- Labile
- Turaren daki
- Madubi
- Matajin kai
- Kayan kwaliya (musanman dakin mata)
- Mai na shafawa
- Magogi (brush)
Auna fahimta
- Lissafa ababen da ake amfani dasu a daki guda hudu (4)
- A tsarin gidan bahaushe ya soma da me?
Jinga: Rubuta ababen da ku ke amfani dasu a aji
Week 2
Kayakin amfani a tsakar gida
- Taburma
Ana amfani da taburma a tsakar gida sabida a huta.
- Kujerar zama
Ana amfani da kujera sabida zama ayi fira a tsakar gida musanman idan bako ko baki su ka zo gaisuwa.
Kayakin amfani na yin girki
- Murhu
- Tukunya
- Kwanuka
- Muciya
- Fanteka
- Matsami
- Faranti
- Kasko na yin masa
Kayakin da ake amfani dasu wajen girki
Auna fahimta
1)Bada misalan ababe guda biyu da ake amfani dasu a tsakar gida da amfanin su.
Jinga: Rubuta amfanin waddanan abubuwan wajen girki.
i)Murhu
ii)Tukunya
iii)Kwanuka
iv)Muciya
v)Fanteka
vi)Matsami
vii)Faranti
viii)Kasko na yin masa
Week 3 Topic: Furuci
Ma’anar furuci
Kalmar furuci na nufin daya daga cikin bangarorin illimi kimiyyar harsuna. Shi kansa wannan bangare na nazarin furuci yana da nasa kashe-kashen da yawa. Akwai kashin da ke duba yadda ake furta bakake da wasula da sauran. A nan, muna duba yadda ake sarrafa gabubban furuci ke nan.
Akwai kuma kashin da ke duba yadda kunne da kwakwalwa ke taimakawa wajen sauraron abin da ke furta. Haka kuma akwai kashin da ke duba yadda su irin wadannan sautuka suke karakaina a igiyai iska.
A wannan darasi, za mu fi mai da hankali ne ga kashin da ke duba yadda ake yin furuci da gabubban furuci (wato mafurta ) da yanayin yin furuci da murya da kuma tafarkin fitar Magana.
Tafarkin fitar magana
A duk lokacin da mutum ya yi Magana , yana amfani da iska ne da yake shaka kuma ya fitar lokacin da yake numfashi.
A yanayin kowani furuci, ita irin wannan iska ana iya amfani da ita ne a wurare uku a tafarkinta. Wadannan wurare kuwa sune
(1.)huhu
(2.)makwallato,
(3.) beli.
Week 4 Topic: Gabobin furuci.
- Lebba Kirjin harshe
2.Hakora 10. Doron harshe
3.Hanka 11.Tushen harshe
- Ganda 12.Mararraba
- Handa 13.Tantanin makwallato
6.Beli 14. Kogon harshe
7.Tsinin harshe 15.zakaran wuya
8.Gaban harshe 16.Gangar makwallato
Auna fahimta.
- Lisafa gabobin furuci guda hudu(4)
- Ba da misalin furuci wada lebbe yake motsi
Week 5. Topic: Gabobi masu motsi
Mafurta
Abin da muke nufi da mafurta a nan, su ne gabobin jiki da ake amfani das u wajen yin furuci. Su irin wadannan mafurta sun kasu kasha biyu. Akwai kafaffu, wato wadanda ba sa motsi, ko kuma motsinsu kadan ne, akwai kuma masu motsi. Yawanci mafurta masu motsi,su ne a sassan kasa idan aka dubi surar tafarkin fitar Magana da ke kasa. Kafaffun, yawanci duk a sama suke. Ga sauran mafurtan da muke amfani da sun an wajen yin furuci.
Murya: A koyaushe aka yi furuci iskar Magana sai ta bi ta makwallato. Idan lokacin wucewar iskar, makwallato a matse yake, furucin yana fitowa da zaki. Wannan shi ake kira zoza. Idan kuwa a bude makwallato yake sai furuci ya fita ba zaki. Wato ba shi da zoza.
Bakake marasa zoza sun hada da p’ s’ da t’ amma b’ da z’ da d’ masu zoza ne. idan kasa yatsunka a kunnuwanka kuma da kan zakaran wuyanka, za ka ji wani diri, idan bakin da ka furta ta mai zoza ne.
Gabobi masu motsi
- Tsinin harshe
- Gaban harshe
- Kirgin harshe
- Doron harshe
- Lebba
Motsin Lebba
A wajen furta wasula, lebba suna da muhimmanci kwarai da gaske. A wajen furta wasulan da ake furtawa a kuryar harshe amma kuma bayan harshe ya yi doro ko ya kusanci yin doro, lebban mutum sukan yi kamar an yi da’ira da su ne. A nan akan ce lebban suna zumbure misali O, U. wajen furta wasulan da ake fada kusa da kuryar harshe kuma amma lokacin da harshe ya kwanta, lebban sukan bude sosai ne watau su wangame; misali, wajen furta a. Haka kuma wajen furta wasulan da ake fada a gaban baki watau da tsinin harshe, lebban suka dan taba ne, watau sun zama a shake. Misali e, i.
Motsin harshe
A bayannin motsin lebba, mun rigaya mun dan taba irin motsin da harsh eke yi wajen furta wasula. Watau yana iya yiwo gaban baki, kuma ya yi doro misali wajen furta I dogo ko gajere. Haka kuma harshen yana iya yiwo gaba, amma ba zai yi toroko ba, misali wajen furta e, dogo ko gajere.
Misalan furucin (a)/O,U/
(b) /a/
(C) /e,i/
Tambayoyin auna fahimta.
1.)Wadanne mafurta ne muhimmai wajen furucin wasula?
2.)Me ya sa ake kiran wasu mafurtan kafaffu wasu kuma masu motsi.
Week 6. Topic: Gabobi marasa motsi.(kafaffu)
1). Hakora
2).hanka
3.) handa
4.) ganda
Furucin bakake:
Murya: Bakaken hausa sun kasu kashi biyu wajen murya. Akwai masu zoza akwai kuma marasa zoza. Misali, bakaken p da s da t ba su da zoza: amma b da z da d masu zoza ne. idan ka sa yatsunka a kunnuwanka kuma da kan zkaran wuyanka, za ka ji wani diri, idan bakin da ka furta mai zoza ne.
Ga dai wasu nan daga cikin irin yanayin da mafurta kan shiga wajen yin furuci bakake tare da sunayen irin bakaken da akan furta ta haka din.
Muryan fitar da bakake
- Katsewa : Idan har mafurtan suka taba juna to an katse iskar furuci ken an. Idan iska mai fitowa waje ce sak, ana kiran bakake da ake samu ta haka,yan Bindiga . idan kuma iskar mai shiga ciki ce to ana kiran su hadiyau.Ga yan misali.
a)Yan Bindiga b, d, g, k
b)Tunkudau K
- c) Hadiyau b, d
2) Tsukewa: Idan kuma mafurtan sun kusanci juna ne kawai ta yadda tilas iskar ta fita tare da firgagi (wato zuza.) kamar idan mutum zai hura wuta to ana kiran wadannan bakake ‘Yan zuza’ misali kamar s da z da sh da f.
3) katsewa da tsukewa.: Akwai wani yanayin furuci kuma da a lokacin yin sa, mafurtan sukan taba juna sa’annan su ware amma su zama kamar a tsuke. Bakaken da aka furtawa ta haka ana kiransu Yan Atishawa, domin kamar atishawar ake yi lokacin furta su. Misali, ts da j
Mafurta
Tilo( singular) | Jam’i(plural) | Bakake |
Balebe | Lebawa | B,b,m,f,w |
Bahanke | Hankawa | D,t z, s,ts,r,l, n |
Gandawa | Bagande | J,c,sh ,y |
Handawa | Bahande | K,g,k |
Yan makwallato | Dan makwallato | H,?. |
Auna Fahimta:
- Lisafa gabobi marasa motsi guda uku.
2.Muryar furta baki iri nawa muke dashi?
3.A wani mafurci ake furta ‘b’
Aiki : Danganta wadannan bakake da wuraren furta su.
Misali:
b——————–à lebe
c——————-àganda
1) g
2)r
3.)j
4.)n
5.)h
Week 7. Topic: Ma’anar ginin kalma
A darasin da gabata an yi bayani akan furucin bakake. Idan aka duba misalan furuci bakake da misalan furucin wasula, za a tarar cewa babu wata ma’ana da kowannensu yake bayarwa. Watau misali ba za a iya cewa bakin ‘g’ ko m yana da wata ma’ana ba. Haka ma wasalin o ko u da duk sauransu ba su da wata ma’ana tasu ta kansu su kadai.
Idan mai Magana yana so ya yi wani furuci mai ma’ana, to dole ne ya harhada wasu bakake tare da wasula,Wanda yake bada ma’ana, shi ake kira kalma. Ga misalan kalmomi nan :
1.Yaro
2.Malama
3.lokaci
4.Littafi
5.Agogo
6.Ruwa
7.Sanyi
Da zarar an furta kowanne daga cikin taron bakake da wasullan nan, za aji suna Magana ne a kan wani abu wanda za a iya gani ko ji,ko za a iya tunaninsa. Watau ya ba da ma’ana kenan. Saboda haka, ya zama kalma
Kirar kalma
Idan aka dubi misalan da aka bayar a nan, za a ga wata Kalmar ta tafi wata tsawo. Abin da ya kawo haka kuwa shi ne, wata ma’anar takan bukaci taron bakake a wasula kadan wata kuwa takan bukaci taron bakake da wasula mai yawa. Kwatanta yawan bakake da wasula da ke cikin “Yaro” da wadanda taron bakake da wasulansu suka bambanta.
Haka kuma za’a iya karya kalma gaba-gaba, dangane da tsawonta. Watau gajeriyar kalma, zai kasance tana da gabobi kadan ke nan. Doguwa kuma tana da gabobi da yawa. Dubi wannan misali.
Masara
Ma/ sa/ra (gaba uku)
Yaro
Ya/ro (gaba biyu)
Makaranta
Ma/ka/ran/ta (gaba hudu)
Week 8.
Amfanin kalma
a.)Da taimakon kalmomi ne za mu iya hira tsakaninmu,
b.)ko mu yi tambaya
- c) ko malami ya ba da umurni.
Duba wadannan misalai.
- Audu ina za ka ?
- Malam, yaya sunan wannan
- .To yara, kowa ya bude shafi na goma.
A misali na farko, yara ne guda biyu suke Magana da juna.A misali na biyu yaro ne yake wa malami tambaya. A na uku kuwa malami ne yake ba yara umurni.
Wadannan misalai sun nuna mana cewa, da taimakon kalmomi ne muke iya tada Magana mai ma’ana.
Auna fahimta.
- Kawo kalmomi naka guda uku (3)
- Amfanin kalma nawa aka nuna a wannan darasi? Bayyana su.
Akin karshen mako
- Wane abu ne sais a a gane cewa wannan taron baki da wasali “kalma” ce.
- Karya wadannan kalmomi gaba-gaba.
i)hudu
ii)gida
iii)madara
iv)gishiri
v)makamashi
week 9. Ma’anar ginin kalma
A darasin da gabata an yi bayani akan furucin bakake. Idan aka duba misalan furuci bakake da misalan furucin wasula, za a tarar cewa babu wata ma’ana da kowannensu yake bayarwa. Watau misali ba za a iya cewa bakin ‘g’ ko m yana da wata ma’ana ba. Haka ma wasalin o ko u da duk sauransu ba su da wata ma’ana tasu ta kansu su kadai.
Idan mai Magana yana so ya yi wani furuci mai ma’ana, to dole ne ya harhada wasu bakake tare da wasula,Wanda yake bada ma’ana, shi ake kira kalma. Ga misalan kalmomi nan :
1.Yaro
2.Malama
3.lokaci
4.Littafi
5.Agogo
6.Ruwa
7.Sanyi
Da zarar an furta kowanne daga cikin taron bakake da wasullan nan, za aji suna Magana ne a kan wani abu wanda za a iya gani ko ji,ko za a iya tunaninsa. Watau ya ba da ma’ana kenan. Saboda haka, ya zama kalma
Kirar kalma
Idan aka dubi misalan da aka bayar a nan, za a ga wata Kalmar ta tafi wata tsawo. Abin da ya kawo haka kuwa shi ne, wata ma’anar takan bukaci taron bakake a wasula kadan wata kuwa takan bukaci taron bakake da wasula mai yawa. Kwatanta yawan bakake da wasula da ke cikin “Yaro” da wadanda taron bakake da wasulansu suka bambanta.
Haka kuma za’a iya karya kalma gaba-gaba, dangane da tsawonta. Watau gajeriyar kalma, zai kasance tana da gabobi kadan ke nan. Doguwa kuma tana da gabobi da yawa. Dubi wannan misali.
Masara
Ma/ sa/ra (gaba uku)
Yaro
Ya/ro (gaba biyu)
Makaranta
Ma/ka/ran/ta (gaba hudu)
Week 10.
Amfanin kalma
a.)Da taimakon kalmomi ne za mu iya hira tsakaninmu,
b.)ko mu yi tambaya
- c) ko malami ya ba da umurni.
Duba wadannan misalai.
- Audu ina za ka ?
- Malam, yaya sunan wannan
- .To yara, kowa ya bude shafi na goma.
A misali na farko, yara ne guda biyu suke Magana da juna.A misali na biyu yaro ne yake wa malami tambaya. A na uku kuwa malami ne yake ba yara umurni.
Wadannan misalai sun nuna mana cewa, da taimakon kalmomi ne muke iya tada Magana mai ma’ana.
Auna fahimta.
- Kawo kalmomi naka guda uku (3)
- Amfanin kalma nawa aka nuna a wannan darasi? Bayyana su.
Akin karshen mako
- Wane abu ne sais a a gane cewa wannan taron baki da wasali “kalma” ce.
- Karya wadannan kalmomi gaba-gaba.
i)hudu
ii)gida
iii)madara
iv)gishiri
v)makamashi
Week 11. Bita a kan darasunnan sashe duka
Week 12. Jarabawa.